Kotun Kano ta hukunta matashi dan shekara 20 daya zakke ma yarinya yar shekara 3

Kotun Kano ta hukunta matashi dan shekara 20 daya zakke ma yarinya yar shekara 3

Wata babbar kotun majistri dake garin Kano ta aika da Khalid Abdullahi mai shekara 20 zuwa gidan Kurkuku bisa tuhumar zargin da ake masa na yi ma wata karamar yarinya yar shekara 3 fyade a jahar Kano.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito wannan matashi yana zama ne a unguwar Yankaba dake cikin garin Kano, kuma a yanzu haka ana tuhumarsa da laifin aikata fyade wanda ya saba ma sashi na 283 na kundin dokokin hukunta manyan laifuka.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makarantar Firamari a Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dansanda mai kara, Inspekta Pogu Lale ya bayyana ma kotu cewa wani mutumi mai suna Mohammed Saddam Badawa ne ya kai kara zuwa ofishin Yansandan Bompai a ranar 22 ga watan Satumba.

“Da misalin karfe 2 na ranar 21 ga watan Satumba ne ne Khalid ya shigar da karamar yarinyar zuwa dakin yayarsa dake wani gidan sama a unguwar Badawa inda ya yi mata fyade wanda hakan ya janyo samun rauni ga yarinyar.” Inji ta.

Sai dai wanda ake kara ya musanta aikata wannan laifi, daga bisani bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu ne sai Alkalin kotun Muhamamd Jibril ya bada umarnin a daure masa Khalid a gidan yai har zuwa ranar 28 ga watan Oktoba da za’a cigaba da sauraron shari’ar.

A wani labarin kuma, ministan harkokin noma a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Sabo Nanono ya kara tabbatar da cewa akwai inda ake sayar da abincin N30 a koshi a jahar Kano, kuma duk mai jayayya da hakan yazo zai kaishi wajen.

A makon data gabata ne dai Nanono ya fara furta wannan magana, inda yace babu yunwa a Najeriya, wannan maganan ta janyo cecekuce a tsakanin yan Najeriya, musamman a shafukan sadarwar zamani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel