Kashi 14% na mutanen duniya masu shan 'Taramol' da 'Kodin' yan Najeriya ne - Binciken Janar Buba Marwa

Kashi 14% na mutanen duniya masu shan 'Taramol' da 'Kodin' yan Najeriya ne - Binciken Janar Buba Marwa

Mutum daya cikin kowani mutane bakwai masu shekarun 15 zuwa 64 a Najeriya na amfani kwaya akalla guda daya, a cewar shugaban kwamitin yaki da ta'amuni da muggan kwayoyi a Najeriya, Janar Buba Marwa.

Hakan ya banbanta da binciken masu ta'amuni na duniya da aka samu cewa kowani mutum daya cikin mutane ashirin na ta'amuni na kwayoyi.

Ya bayyana hakan ne a lakcan kaddamar da kungiyar kwararru masu warakar da ta'amuni da kwaya wato Society of Substance Use Prevention and Treatment Professionals (ISSUP) a Abuja ranar Talata.

Janar Marwa ya ce mutum daya cikin biyar na masu amfani da muggan kwayoyi a Najeriya na fama da cutar kwakwalwa. Hakan ya banbanta da binciken masu ta'amuni na duniya da aka samu cewa mutum daya cikin mutane 11 ne ke da cutar kwakwalwa.

Ya ce yawan yan Najeriya kashi 3% na kawai na yawan duniya amma kashi 6% masu shan wiwi a duniya a Najeriya ne.

KU KARANTA: Manoma sun fi kowa yin jima'i - Binciken kasar Ingila

Ya kara da cewa kashi 14% na yawan masu amfani da muggan kwayoyi, hakan ya sa Najeriya na cikin kasashen duniya mafi yawan masu amfani da Taramol da Kodin.

A wani labarin daban, Masu shan shayi akai-akai sun fi lafiyan kwakwalwa bisa ga sabon binciken kasar Singapore ya bayyana.

Farfesa Feng Lei, kwararren malamin lafiyar kwakwalwa a tsangayar ilimin magani na Yong Loo dake jami'ar kasa ta Singapore ya bayyana cewa shan shayi na da muhimmanci ga lafiyar kwakwalwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel