Kai rayayyen gwarzo ne, Buhari ga Gowon yayinda ya cika shakara 85 a duniya

Kai rayayyen gwarzo ne, Buhari ga Gowon yayinda ya cika shakara 85 a duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Janar Yakubu Gowon murna gabanniin zagayowar ranar haihuwarsa karo na 85 wanda zai kama a ranar 19 ga watan Oktoba, inda ya bayyana shi a matsayin gwarzo kuma alama na hadin kan kasa.

Shugaba Buhari, a wani jawabi daga mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Mista Femi Adesina a Abuja, a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, ya tabbatar da cewar tsarin shugabanci, hikima da nagarta irin na Gowon shine ya cigaba da dorar da kasar a matsayin guda.

Shugaban kasar ya jinjinawa tsohon Shugaban kasar na mulkin soja, inda ya bayyana shi a matsayin Shugaban kasar Najeriya mafi karancin shekaru tun bayan samun yanci, kuma mai imani da tawakkali ga Allah sannan mai burin ganin cigaban kasar.

A cewarsa, jigon kasar ya gina tubali mai karfi ta yadda kasar za ta yi karko, tare da samar da hukumomin tarayya da kuma aiwatar da manufofi masu ma’ana kamar irin su shirin bautar kasa wato NYSC.

KU KARANTA KUMA: Idan muka yi nasara wajen gina ababen more rayuwa, yan Najeriya za su mayar da hankali ga harkokin gabansu - Buhari

Ya bayyana cewa shirin na cigaba da tabbatar da kudirin dake tattare da kafa shin a kawo hadin kai, aminci da kuma ba matasa yan Najeriya daman a tsawon rayuwarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel