Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun tarwatsa dandazon 'ya shi'a da suka fito zanga-zanga a Abuja

Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun tarwatsa dandazon 'ya shi'a da suka fito zanga-zanga a Abuja

Yanzun nan muke samun labarin jami’an ‘yan sanda a Abuja sun yi arangama da ‘yan shi’a masu zanga-zanga a kan lallai sai an saki shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky.

An soma zanga-zangar ne a kan titin Sultan Abubakar dake Abuja da misalin karfe 1:55 na ranar Juma’a 18 ga watan Oktoba.

KU KARANTA:Rufe kan iyaka: Ba munyi ba ne domin mu matsawa wata kasa, FG ta fadawa Ghana

Gungun masu zanga-zangar rike suke da tutoci baka da ja inda kuma suke ihu suna fadin “Labbaika yah Hussaini, a sako mana Zakzaky”. A yayin da ‘yan shi’a ke cigaba da yin tattaki a bisa titin kwatsam sai ‘yan sanda suka soma sake albarushi a saman iska.

Haka kuma ‘yan sandan sun harba barkonon tsohuwa wato tear gas. Tuni masu zanga-zangar suka fara guduwa domin neman wurin fakewa tare da dandazon jama’ar da suke dawowa daga sallar juma’a.

https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/358283-breaking-gunshots-in-abuja-as-police-disperse-protesting-shiites.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel