Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makarantar Firamari a Kaduna

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makarantar Firamari a Kaduna

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutum guda biyo bayan wani mummunan hari da wasu miyagu yan bindiga suka kai a garin Birnin Gwari, cikin karamar hukumar Birnin Gwarin jahar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kaakakin rundunar, DSP Yakubu Sabo ne ya tabbatar da haka a ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba, inda yace yan bindigan sun kai farmakin ne da misalin karfe 11: 30 na safiyar Laraba a wani gidan mai dake kauyen Doka.

KU KARANTA: Janyewa/neman uzuri wurin Sanata Babba Kaita

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito DSP Sabo yace baya ga kisan mutum daya, yan bindigan sun yi awon gaba da wani mutumin, amma yace har yanzu basu tabbatar da mutumin da aka yi garkuwan da shi ba, amma dai jama’an yankin sun ce Malam Abdulhafiz Abdullahi ne, shugaban makarantar firamari ta Dangamji.

A cewar DSP Sabo, mutumin da yan bindigan suka kashe sunansa, Bashir Tanimu, sa’annan ya gargadi jama’a daga yada jita jita a kan abin da basu da tabbaci a kansa saboda matsalar da hakan ka iya haifar ma tsaro, daga bisani kuma ya tabbatar da manufar rundunar na kawar da ayyukan yan bindiga a jahar.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagun yan bindiga sun kaddamar da farmaki a kauyen kadobe dake cikin garin daddara na karamar hukumar Jibiya ta jahar Katsina, inda suka yi awon gaba da tarin dabbobi da suka kai 228.

Rundunar Yansandan jahar Katsina ce ta tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da kaakakinta, Gambo Isah ya fitar, inda yace da misalin karfe 5:51 na asubah na daren Juma’a suka samu kira daga kauyen game da aukuwar harin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel