Tsuguni bata kare ba! Gungun yan bindiga sun tarkata dabbobin jama’a a jahar Katsina

Tsuguni bata kare ba! Gungun yan bindiga sun tarkata dabbobin jama’a a jahar Katsina

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun kaddamar da farmaki a kauyen kadobe dake cikin garin daddara na karamar hukumar Jibiya ta jahar Katsina, inda suka yi awon gaba da tarin dabbobi da awaki da suka kai 228.

Rahoton gidan talabijin na Channels ta ruwaito rundunar Yansandan jahar Katsina ce ta tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da kaakakinta, Gambo Isah ya fitar, inda yace da misalin karfe 5:51 na asubah na daren Juma’a suka samu kira daga kauyen game da aukuwar harin.

KU KARANTA: Janyewa/neman uzuri wurin Sanata Babba Kaita

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gambo yace ba tare da bata lokaci ba rundunar hadaka ta jami’an tsaro dake gudanar da sintiri a yankin suka garzaya kauyen, inda suka yi ma yan bindigan kawayan, nan aka yi ta musayar wuta.

“Daga karshe zaratan jami’an tsaron sun samu galaba a kan yan bindigan, sa’annan suka kwato dabbobin da suka tarkata da fari da suka hada da shanu 99, awaki 128, da kuma jaki guda daya.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yace a yanzu haka rundunar ta kaddamar da bincike a kan aukuwar lamarin domin bin bankado duk inda yan bindigan suka shiga, sa’annan yace an mika dabbobin ga mai su, wani mutumi mai suna Tasi’u Hamisu.

A wani labarin kuma, jami’an rundunar Yansandan Najeriya, reshen jahar Ribas Fatakwal sun samu nasarar halaka wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da ake kira da suna Agabiseigbe.

Barawon ya yi kaurin suna wajen tare babbar hanyar Owerri zuwa Fatakwal inda yake sace mutane, tare da yin garkuwa dasu har sai an biyashi kudin fansa, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar, DSP Nnamdi Omoni ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel