Rufe kan iyaka: Ba munyi ba ne domin mu matsawa wata kasa, FG ta fadawa Ghana

Rufe kan iyaka: Ba munyi ba ne domin mu matsawa wata kasa, FG ta fadawa Ghana

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce babu wani dalilin takura ko matsi ga wata kasa da ya sanya ta rufe kan iyaka. Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ne ya fadi wannan maganar.

Mr Geoffrey Onyeama ya fadi wannan maganar ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba a Abuja a lokacin da yake ganawa da ministocin kasar Ghana guda biyu.

KU KARANTA:An bada labari game da rayuwar tsohon Shugaban kasan Najeriya cikin wani sabon fim

Ministocin da suka halarci zaman daga kasar gane su ne, Shirley Botchwey da kuma Alan Kyerematen ministan kasuwanci. Onyeama ya sanar da su rufe kan iyakar bai shafi takurawa ko wace kasa ba.

A cewarsa Najeriya, a matsayinta na daya daga cikin kasashen dake kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ta ECOWAS ta na matukar girmama dokokin kungiyar.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa, mutane za su cigaba da shige da fice da kayayyakinsu a kan iyakokin Najeriya, inda ya ce rufe kan iyakar anyi shi ne domin takaita ayyukan miyagun mutane.

Haka kuma, ya ce Najeriya za ta duba korafin kasar Ghana tare da yin abinda ya dace game da shi cikin gaggawa ba tare da an samu tsaiko ba.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, wani marubuci da kuma bayar da umarnin fina-finan turanci ya shirya wani sabon fim mai suna ‘Badamosi’ inda yake bada tarihin rayuwar tsohon Shugaban kasar Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida wato IBB.

A cikin shirin marubucin ya tabo abubuwa da dama daga rayuwar IBB, inda ya soma da yarintarsa har zuwa lokacin da ya zama Shugaban Najeriya.

https://www.channelstv.com/2019/10/17/border-closure-no-country-is-targeted-nigerian-govt-tells-ghana/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel