Idan muka yi nasara wajen gina ababen more rayuwa, yan Najeriya za su mayar da hankali ga harkokin gabansu - Buhari

Idan muka yi nasara wajen gina ababen more rayuwa, yan Najeriya za su mayar da hankali ga harkokin gabansu - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Najeriya a matsayinta na kasa Allah ya rigada ya kadarce ta da zama mai inganci domin cike take da al’umma masu kwazon kasuwanci da burin bunkasa ta.

Buhari ya fadi hakan ne a wasu jerin jawabai da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @MBuhari a ranar Juma’a, 18 ya watan Oktoba.

Shugaban kasar ya bayyana cewa gina ababen more rayuwa ya kasance daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba kamar yadda ya bayyana cewa yan Najeriya da dama “Za su mayar da hankali ya harkokin gabansu” sannan “ba za su damu da ko wanene a kan mulki ba” idan gwamnatinsa tayi nasara a wajen gina ababen more rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Ba lafiya: Bidiyon yadda tankar mai ke ci da wuta a hanyar babban titin Lagas-Ibadan

“Wannan ne dalilin da yasa gina ababen more rayuwa zai cigaba da kasancewa daya daga cikin abubuwan da zamu fara mayar da hankali akai. Ya zama dole kuma zamu sake rubutu labari, ga wannan kasa tamu mai albarka. Na so ace muna da kudade fiye da haka, kuma muna aiki akan haka, amma muna iya bakin kokarinmu da kudaden da muke dasu a yanzu,” inji shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel