Sojin Najeriya sun kwato manoma 3 tare da kashe dan ta'adda daya a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Sojin Najeriya sun kwato manoma 3 tare da kashe dan ta'adda daya a hanyar Kaduna zuwa Abuja

- Rundunar sojin Najeriya ta Operation Thunder Strike sun kwato wasu manoma 3 daga hannun masu garkuwa da mutane

- Manoman an sacesu ne a ranar Laraba lokacin da suke aikinsu a gona a kauyen Maro

- Rundunar sojin sun hallaka dan ta'adda daya inda suka raunata sauran kafin su tsere

Rundunar sojin Najeriya ta 'Operation Thunder Strike' sun tseratar da wasu kauyawa uku da aka yi sacesu a gonarsu a ranar Laraba a kauyen Maro dake babban titin Kaduna zuwa Abuja.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamnatin jihar Gombe zata rage yawan ma'aikatu daga 27 zuwa 21

Mataimakin daraktan hulda da jama'a na runduna ta daya, Col. Ezindu Idimah ya sanar da kamfanin dillancin labarai a Kaduna cewa, a ranar Juma'a ne sojin suka kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen.

"Bayan samun labarai gamsassu akan maboyar 'yan ta'addan, rundunar sun kai samame inda suka yi musayar wuta tare da ceto manoman,"

"Bayan musayar wutar, an kashe daya daga cikin 'yan ta'addan inda sauran suka tsere amma da raunika tare dasu. Tuni aka mika manoman da aka ceto ga iyalansu," in ji shi.

Idimah yace, an samu bindiga kirar AK 47 da kuma alburusai a maboyar tasu.

"Babban kwamandan runduna ta daya ta sojin Najeriya, Maj. Gen. Faruk Yahaya, ya yi kira ga jama'a dasu kai rahoton duk wanda suka gani da harbin bindiga a jiki ga hukumar tsaro mafi kusa don daukar matakin bincike." kamar yadda Idimah yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel