PDP ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan nada wa Aisha hadimai

PDP ta yi wa Buhari wankin babban bargo kan nada wa Aisha hadimai

- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tana son Shugaba Muhammadu Buhari ya zama madubi da na kasa da shi za su rika koyi da shi

- Jam'iyyar adawar ta yi ikirarin cewa nadin hadimai da shugaban kasar ya yi wa ofishin First Lady ya sabawa ikirarin da ya ke yi na rage kashe kudade a gwamnati

- Jam'iyyar kuma ta nemi shugaban kasar ya rage adadin jiragen sama da ofishinsa ke amfani da su

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi ikirarin cewa naddin sabbin hadimai da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa ofishin First Lady Aisha Buhari ya ci karo da alkawarin da ya yi a baya na rage kashe kudaden gwamnati.

A sakon da mai magana da yawunta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar, jam'iyyar adawar ta bukaci shugaban kasar ya rika aiki da abinda ya ke horar wasu su aikata na yin takatsantsan wurin kashe kudaden gwamnati ta hanyar ja kunnen ministocinsa da sauran masu mukami.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: FG da Kungiyar Kwadago sun cimma matsaya kan sabon albashi

PDP ta yi ikirarin cewa babu wata bukatar ofishin shugaban kasa ta tallafawa ofishin First Lady da hadimai duba da cewa a baya an ruwaito cewa Shugaba Buhari ya ce ba zai ware wani kudi don ofishin First Lady ba.

Jam'iyyar ta PDP ta ce, "Jam'iyyar PDP tana bukatar shugaban kasa ya yi wa 'yan Najeriya bayanin dalilin da yasa ya saba alkawarin da ya dauka a baya."

Ta kuma bukaci shugaban kasar ya fara rage adadin jiragensa da mutanen da ya ke diba a tawagarsa idan zai fita kasashen waje.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin hadimai shida domin ofishin First Lady ta Najeriya, Aisha Buhari.

An tabbatar da nadin hadiman ne cikin wata sa sanarwa da direktan yada labarai na First Lady, Suleiman Haruna ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel