Kashi 80% na kudin da muke amfani da shi daga badakalar Abacha ne - Maryam Uwais

Kashi 80% na kudin da muke amfani da shi daga badakalar Abacha ne - Maryam Uwais

Mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan shirin jin dadin al'umma NSIP, Hajiya Maryam Uwais, ta bayyana cewa kashi 80% na kudaden da suke rabawa jama'a daga kudin babakeren Abacha ne.

Hajiya Uwais ta bayyana hakan ranar Alhamis a wani taron horo da wayar da kai kan bibiyan kudaden sata da dukiyoyi.

An gudanar da wannan taro ne birnin tarayya Abuja inda kungiyoyin HEDA, Gidauniyar MacArthur, The Corner House, Finance Uncovered, PTCIJ da Kent Law School suka dau nauyi.

KU KARANTA: An karrama jarumi Ali Muhammad Nuhu a kasar Indiya

Tace: "Kudin shirin jin dadin al'umma daga bankin duniya da badakalar Abacha yake. Kashi 20 na bashin da gwamnati ke karba daga bankin duniya ake bamu, sannan sauran kashi 80 daga badakalar Abacha."

Ta ce sauran kashi 20% din daga bankin duniya yake.

Shirin jin dadin al'ummar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kawo ya kunshi shirin N-Power, GEEP, Ciyar da dalibai makarantun firamare da sauransu.

Ta ce mutanen da ke amfana da wannan shiri suna kokari kwarai da gaske.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel