Abokin kowa: 'Yan sanda sun tilasta budurwa ta nuna lasisin karenta ko su kamata

Abokin kowa: 'Yan sanda sun tilasta budurwa ta nuna lasisin karenta ko su kamata

- Wata mata ta bayyana yadda ta sha fama da 'yan sanda a lokacin da suka tare ta zasu duba motar ta

- Matar ta bayyana cewa bayan sun gama caje motar ta tsaf basu ga wata matsala ba sai suka dawo suke tambayarta akan ta kawo musu lasisin karenta da suka gani a cikin motar

- Matar ta tambayi dan sandan ya nuna mata inda a doka aka ce sai mutum ya nuna lasisin kare a Najeriya

Wata budurwa ta wallafa wani rubutu a shafinta na sadarwa cikin bacin rai, inda tayi bayanin yadda tayi ta fama da 'yan sanda bayan sun tare ta a wajen bincike na kan tintuna.

A cewar matashiyar budurwar, 'yan sandan sun bukaci ta bayar da racitin karenta bayan sun gama binciken kwa-kwaf a jikin motar ta sun kasa gano matsala ko guda daya a jiki.

Ga abinda budurwar ta rubuta:

"'Yan sandan Najeriya mahaukata ne.

"Shin ya kamata dan sanda ya tsare ka saboda ka dauki kare a motar ka?

"Shin akwai wani wuri da ya nuna cewa sai ka yiwa kare lasisi a Najeriya?

KU KARANTA: Wannan abin kunya da yawa yake: Uba na kiran samarin 'ya'yansa ya sanya suyi zina da su shi kuma yana gefe yana kallo

"Wani dan sanda ya tare ni a hanya, wai ya nemi na bashi lasisin karena, har yake zargina da cewa wai sato karen na, na tambayeshi ya nuna mini a cikin dokar su ta 'yan sanda inda aka ce su dinga tambayar mutane lasisin kare.

"Bayan nayi masa wannan tambayar ya kasa cewa komai sai ya kyaleni na wuce.

"Bai ga matsala ko daya a jikin motata ko takarduna ba, shine yasa ya dawo kan kare domin ya samu hanyar cin kudi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel