Ba lafiya: Bidiyon yadda tankar mai ke ci da wuta a hanyar babban titin Lagas-Ibadan

Ba lafiya: Bidiyon yadda tankar mai ke ci da wuta a hanyar babban titin Lagas-Ibadan

An gano wata motar tabka tana ci bal-bal da wuta a hanyar babban titin Lagas zuwa Ibadan a safiyar ranar Juma’a, 18 ga watan Oktoba.

A cewar wani mai amfan da shafin Twitter, Jojo Amiegbe, wanda ya wallafa bidiyon kunar takar a shafin sadarwar, tankar ya kama da wuta ne kafin sansanin Redeemed da ke hanyar na Lagas.

A cikin bidiyon, ba a ga jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ba a wajen da lamarin ya afku.

Hukumar da ke kula da hana afkuwar hatsaruruka ta tabbatar da fashewar tankar, jaridar Punch ta ruwaito.

Wanan shine karo na uku da ake samun lamarin tashin taka a ranar yau Juma’a.

Kalli bidiyon a kasa:

A wani lamari makamancin wannan, mun ji cewa wata tanka dauke da man fetur da sake kamawa da wuta a kan titin Enugu-Onitsa kusa da gidan man fetur na Bessoy a Onitsha a jihar Anambra.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Dickson ya gana sa Buhari, ya ce APC ba za ta shugabancin Bayelsa ba

Wannan na zuwa ne bayan mummunan gobarar da wata motar dakon man fetur ta janyo a kasuwar Ochanja da Upper Iweke kimanin awanni 48 da suka gabata.

The Nation ta ruwaito cewa babban motar da ke dauke da man fetur ya fadi a tsakiyar titi inda man da ya ke dauke da shi ya kwarare cikin magudanan ruwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel