Gwamna Dickson ya gana sa Buhari, ya ce APC ba za ta shugabancin Bayelsa ba

Gwamna Dickson ya gana sa Buhari, ya ce APC ba za ta shugabancin Bayelsa ba

- Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja

- Dickson yace jam’iyyar Peoples Deomcratic Party (PDP) ta lashe zabe mai zuwa ta gama a jihar

- A cewarsa jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna, David Lyon, ba za su iya shugabancin jihar Bayelsa ba

Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa a jiya Alhamis, 17 ga watan Oktoba, ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Da yake Magana bayan ganawar da suka yi cikin sirri, Dickson yace jam’iyyar Peoples Deomcratic Party (PDP) ta lashe zabe mai zuwa ta gama a jihar.

Yace jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna, David Lyon, ba za su iya shugabancin jihar Bayelsa ba.

Gwamnan ya ce har yanzu yana jagorancci a kokarin da suke na ganin sun lallashi fusatattun mambobin jam’iyyar biyo bayan sakamakon zaben fidda gwani na PDP.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi umurnin binciken hukumar raya Niger Delta, ya ce bai san inda dukka kudaden suka shiga ba

Ya yi kira ga hadin gwiwa tsakanin shi a matsayinsa na Shugaban PDP da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva a matsayinsa na Shugaban APC dmin cimma zaben gwamna na gaskiya da lumana a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel