Janyewa/neman uzuri wurin Sanata Babba Kaita

Janyewa/neman uzuri wurin Sanata Babba Kaita

A ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2019, mun wallafa wani labari mai taken “Girma ya fadi: Wani sanatan jihar Katsina ya sha mari a hannun magoya bayansa.”

Tuni mun gano cewa babu gaskiya cikin wannan labari kuma muna masu janye wannan magana gaba dayanta.

Hakazalika, cikin tawali’u muna bada hakuri ga Sanata Babba Kaita, sanata mai wakiltan mazabar Katsina ta Arewa a majalisar dattawan tarayya wanda wannan labari ya shafa, mabiyansa da al’ummarsa kan duk wani cin mutunci da tsegumin da wannan wallafa ya janyo musu.

Mu na matukar ganin girman Sanata Babba Kaita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel