Wata sabuwa: Gwamnatin jihar Gombe zata rage yawan ma'aikatu daga 27 zuwa 21

Wata sabuwa: Gwamnatin jihar Gombe zata rage yawan ma'aikatu daga 27 zuwa 21

- Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa-Yahaya ya bada umarnin zaftare ma'aikatun jihar

- A da dai jihar na da ma'aikatu 27 ne amma gwamnan ya bada umarnin zabge 6, inda zasu koma 21

- A wani cigaba kuma, gwamnan ya aminta da nada Alhaji Mohammed Manu Malala a matsayin sarkin Yamaltu

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa-Yahaya ya bada umarnin rage yawan ma'aikatun jihar daga 27 zuwa 21.

Mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya sanar da cewa, gwamnan ya nada kwamitin zabtare ma'aikatun tare da tabbatar da cewa zasu yi amfani da umarninsa.

KU KARANTA: Wani kwamishina ya kara barin aiki, ya fadi dalili

A wani cigaba kuma, gwamnan ya aminta da zabar Alhaji Abubakar Ali a matsayin sarkim Yamaltu.

Amincewar shi din na kunshe ne a wasikar da babban sakataren ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar, Alhaji Mohammed Manu Malala yasa hannu.

Malala ya ce, zaben na daga cikin alfarmar da gwamnan ke da ita karkashin shari'a wacce ta bashi damar kirkirar masarautu, dagatai, kauyuka da gundumomin tare da zaba ko sauke sarakai in har hakan ta kama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel