'Yan sanda sun kama 'yan jaridar bogi 3 a Majalisar Tarayya

'Yan sanda sun kama 'yan jaridar bogi 3 a Majalisar Tarayya

Jami'an Rundunar 'Yan sandan Najeriya da ke aiki a harabar Majalisar Tarayya (NASS) a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis sun kama 'yan jaridan bogi uku a harabar majalisar.

An mika wadanda ake zargin; Balarabe Umar, Joseph Andor da Ibrahim Bello hannun DPO na ofishin 'yan sanda na majalisar tarayyar, Mista Abdullahi Sambo.

An gano wadanda ake zargi da yin sojan gona ne jim kadan bayan isowar karamin ministan Albarkarun man fetur, Timipre Sylva majalisar domin ganawa da kwamitin majalisar tarayyar na man fetur don kare kasafin kudin ma'aikatarsa.

Anyi zaman kare kasafin kudin ma'aikatan ne a daki mai lamba 028 a sabon sashin ginin majalisar na tarayyar.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Jim kadan bayan Sylva ya kammala zantawa da manema labarai, an ce 'yan jaridar na bogi sunyi kokarin kusantar ministan suna neman ya basu 'na goro'.

Da aka yi yunkurin hana su sai suka yi barazanar dukkan sauran 'yan jaridar hakan yasa sauran 'yan jaridar NASS suka kira 'yan sanda kuma aka kama su.

Mai magana da yawun Rundunar 'yan sanda ta birnin tarayya Abuja, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar da kama mutanen.

DPO Sambo ya shaidawa The Punch cewa zai yi karin bayani kan mutanen da ake zargin 'yan jaridar bogi ne amma kawo yanzu bai yi karin bayyanin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel