Wani magidanci a Kaduna ya shigar da surukansa kara kotu kan zarginsu da aurar masa da 'yar su mai ciki

Wani magidanci a Kaduna ya shigar da surukansa kara kotu kan zarginsu da aurar masa da 'yar su mai ciki

Wani magidanci mai shekaru 35, Ibrahim Adamu a ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba ya maka surukunsa a gaban alkalin kotun Shari'a da ke jihar Kaduna inda ya ke zarginsu da aura masa 'yarsu bayan sun san tana da cikin shege.

Ana zargin wadanda aka yi karar, Sani Dogon-Zikiri, surukinsa da Laura Sani, surukarsa da laifin yaudara da cin amana.

Wanda ya shigar da karar mazaunin kauyen Rijjana ta bakin lauyansa, Hussaini Yakubu ya shaidawa kotu cewa wadanda akayi karar sun yaudare shi sun aura masa 'yarsu duk da cewa sun san tana dauke a juna biyu.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Mai shigar da karar kuma ya zargi matarsa, Nafisa Sani da hadin baki tare da iyayenta wurin yaudararsa. "Wanda ya shigar da karar da matarsa sunyi gwajin ciki kwanaki kadan bayan daurin aure inda aka tabbatar tana dauke da ciki na makonni biyu kafin auren. Ya tambayi matarsa kuma ta tabbatar masa cikin ba na sa bane," kamar yadda lauyan wanda ya shigar da karar ya shaidawa kotu.

Lauyan wanda ya shigar da karar yana rokon kotu ta tilastawa wadanda aka yi kara su biya N100,000 saboda yaudararsa da su kayi.

Wadanda aka yi kara, ta bakin lauyansu, Abubakar Suleiman sun musanta zargin. Suleiman ya ce kamata ya yi wanda ya shigar da karar ya yi magana a lokacin da ya gano matarsa cewa wai matarsa tana da ciki a maimakon jira har sai da ta haihu.

Lauyan wanda a kayi kara ya ce wanda ya shigar da karar ne mahaifin jinjirin da aka haifa saboda haka babu bukatar a biya shi wani kudi.

Alkalin kotun Mallam Muhammad Adamu-Shehu ya dagae cigaba da sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba domin bawa wanda ya shigar da karar gabatar da shaidunsa a gaban kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel