Yanzu-yanzu: Wata motar dakon man fetur da sake kamawa da wuta a Onitsha

Yanzu-yanzu: Wata motar dakon man fetur da sake kamawa da wuta a Onitsha

Wata tanka dauke da man fetur da sake kamawa da wuta a kan titin Enugu-Onitsa kusa da gidan man fetur na Bessoy a Onitsha a jihar Anambra.

Wannan na zuwa ne bayan mummunan gobarar da wata motar dakon man fetur ta janyo a kasuwar Ochanja da Upper Iweke kimanin awanni 48 da suka gabata.

The Nation ta ruwaito cewa babban motar da ke dauke da man fetur ya fadi a tsakiyar titi inda man da ya ke dauke da shi ya kwarare cikin magudanan ruwa.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane da gidajensu ke kusa da wurin abin ya faru sun fice domin tsoron afkuwar wata gobarar.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

An yi asarar miliyoyin naira tare da gine-gine da kadarori da motocci da wasu abubuwa masu muhimmanci sakamakon gobarar da ta faru a kasuwar ta Ochanja.

Babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar ta yau a lokacin hada wannan rahoton.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, John Abang ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce, "A wannan karon jami'an hukumar kashe gobara sun iso wurin a kan lokaci bayan da jami'ai na suka sanar da su abinda ke faruwa."

Shugaba Muhammadu Buhari da sauran 'yan Najeriya sun jajantawa wadanda gobarar ta kasuwar Ochanja ta shafa inda gwamati tayi alkawarin bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel