An samu naira miliyan 324 a asusun bankin wata mabaraciya

An samu naira miliyan 324 a asusun bankin wata mabaraciya

- Wani bincike ya bayyana yadda mutanen kasar Lebanon suka mayar da wata mabaraciya hamshakiyar mai kudi

- An samu kudi dai sama da naira miliyan dari uku da ashirin da hudu a asusun matar a lokacin da taje zata kwashe kudinta a bankin da take ajiya

- Hotunan matar dai da kuma na katin da take cire kudi sun karade ko ina a shafukan sadarwa na zamani

Tausayi da kirki irin na al'ummar kasa Lebanon ya saka wata mabaraciya ta zama hamshakiyar mai kudi, kamar dai yadda manema labarai suka fitar rahoton a kasar.

Hotunan mabaraciyar mai suna Wafaa Mohammed Awad dana katin kudi na bankin ajiyarta sun karade da yawa daga cikin shafukan sada zumunta na zamani bayan an bayyana cewa mabaraciyar wacce take yin bara a birnin Saida na kasar ta Lebanon ta tara kudi kimanin dalar amurka dubu dari tara, wato kimanin naira miliyan dari uku da ashirin da hudu a kudin Najeriya.

An bayyana cewa matar wacce take ajiye kudin nata a bankin Jamal Trust Bank, za ta samu kudi kimanin fam biliyan daya da miliyan dari biyu da hamsin idan aka canja kudin zuwa kudin kasar ta Lebanon.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Rahama Sadau ta sake jawo kace-nace akan wani hoto da tayi tana sumbatar mace 'yar uwarta

Wannan lamari na matar ya fito fili ne bayan mabaraciyar ta yi kokarin cire kudinta duka daga bankin da take ajiye kudin zuwa wani banki saboda matsalar kudi da bankin nata yake samu.

Hoton katin da take cire kudi dashi a banki wanda ta sanyawa hannu a ranar 10 ga watan Satumba ya karade ko ina a kafafen sadarwa. Wannan ne yake nuni da cewa Awad tafi mutane da yawa da suke bata sadaka arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel