Jama’atu Nasril Islam ta yi magana kan yaran da aka sace daga Kano

Jama’atu Nasril Islam ta yi magana kan yaran da aka sace daga Kano

Kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam tayi kira ga hukumomin gwamnati da nauyin ya rataya a kansu da su gaggauta dawo da yaran nan tara da aka sace daga Kano aka kai su kudancin Najeriya hannun iyayensu da 'yan uwansu a kuma ba su dukkan talafin da suke bukata.

A sakon da sakataren kungiyar, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya fitar a jiya Alhamis kan zargin da ake yi na sace yaran, ya bayyana satar yaran a matsayin "dabbanci, rashin imani ga yara, cin zarafin dan adam kuma abinda ba za a amince da shi ba."

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati ta zurfafa bincike a kan daruruwan karrarakin da aka shigar na bacewar wasu yaran da ake zargin su ma safarar su aka yi zuwa kudancin kasar.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Dakta Khalid ya shawarci iyayen 'yara su rika kare 'ya'yansu daga miyagun mutane.

Sanarwar ta ce, "Ya zama dole a gurfanar da wadanda ke da hannu cikin lamarin gaban kotu kuma a hukunta su kamar yadda doka ta tanada. Za mu cigaba da bibiyar batun domin mu tabbatar an yi adalci.

"Abin takaici da ban tsoro shine yadda mutanen sukayi gaggawar sauya wa kananan yaran sunayensu zuwa na kirista domin su kawar da tarihinsu da dangartakarsu da al'adunsu."

Sanarwar kuma yi yabo da jinjina da Rundunar 'yan sandan Najeriya, da wasu kafafen watsa labarai na kasa da suka taka muhimmiyar rawa wurin watsa labarin wannan zaluncin da kiristoci 'yan kabilar Igbo su kayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel