FG za ta bijiro da haraji na musamman kan kayan zaki

FG za ta bijiro da haraji na musamman kan kayan zaki

Gwamnatin tarayya na tunanin bijiro da haraji na musamman kan kayan zaki irinsu lemun kwalba da sauransu. Ministar kudi, shirye-shiryen kasa da kasafin kudi, Zainab Shamsuna ta bayyana hakan.

Zainab ta bayyana hakan ne a wani hira da tayi da manema labarai ranar Alhamis a taron bankin duniya dake gudana a birnin Washington DC, kasar Amurka.

Ta ce daya daga cikin abubuwan da gwamnati ke tunani kenan domin fadada hanyoyin samun kudin shiga

Ta ce gwamnati za ta tattauna da masu ruwa da tsaki kan ganin yiwuwan hakan.

Tace: "Duk sabon harajin da za'a bijiro da shi sai an yi tuntubi mutane da dama tare da sauye-sauye cikin dokokin da ke kasa ta hanyar kara sabon dokan."

Kayayyakin sun kunshi Coca Cola, Sprite, da Fanta.

KU KARANTA: Wani kwamishina ya kara barin aiki, ya fadi dalili

A bangare guda, Wani faifan bidiyo dake yawo a shafukan ra'ayi da sada zumunta na nuna wani matashi a wata jihar Arewa da ya sayi abinci hannun yarinya a kasuwa amma yaki biyan kudin da ya kamata.

Matashin ya ci abincin N150 amma ya lashi takobin cewa N30 zai biya. Wannan ya biyo bayan jawabin ministan noma, Sabo Nanono, inda ya ce N30 zai kosar da mutum a jihar Kano.

Sabo Nanono ya ce Najeriya a noma abinci mai yawan gaske da zai iya ciyar da kasar baki dayanta, sabanin labarin da wasu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel