Bata suna: Kotu ta bukaci a aje fitacciyar jarumar Kannywood a gidan gyaran hali

Bata suna: Kotu ta bukaci a aje fitacciyar jarumar Kannywood a gidan gyaran hali

- Wata kotun majistare mai zama a Kano ta bada umarnin cigaba da tsare sananniyar tsohuwar jarumar Kannywood, Sadiya Haruna

- Idan bamu manta ba furodusa Isa A. Isa ne ya maka ta gaban kotu sakamakon zarginta da yake da bata masa suna

- Jarumar ta fito kafafen sada zumunta ta sanar cewa sunyi auren mutu'a da furodusan tare da kiransa dan luwadi

Wata kotun majistare mai zama a Kano ta bada umarnin tsare sananniyar tsohuwar jarumar Kannywood din nan, Sadiya Haruna akan zarginta da ake da bata sunan furodusa Isa A. Isa.

An gurfanar da wacce ake zargin ne akan laifin bacin suna wanda yaci karo da sashi ma 391 na Penal Code kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Amma ta musanta laifinta tare da zargin laifin da aka karanto mata.

Lauyan wacce ake zargi, Y. A Sharif ya bukaci kotun da ta bada belinta amma dan sandan mai gabatar da kara, Jacob Yaduma, ya soki bukatar belin.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Yaduma ya ce wacce ake zargin zata iya tsallake belin ko kuma lalata binciken da 'yan sanda ke yi bayan belin.

Mai shari'a, Jastis Muntari Dandago, ya dage bada hukunci akan belin zuwa ranar Juma'a, 18 ga watan Oktoba, 2019.

Alkalin ya bada umarnin cigaba da tsare jarumar a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da za a dubi bukatar belin nata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel