FG za ta bullo da 'rajista' na musamman don talakawan Najeriya

FG za ta bullo da 'rajista' na musamman don talakawan Najeriya

- Gwamnatin Najeriya za ta fito da rajista mai dauke da sunayen talakawa da ke kasar

- Za ayi amfani da rajistan ne wurin aiwatar da shirin gwamnati na tsamo miliyoyin 'yan Najeriya daga talauci

- Gwamnati ta ce akwai irin wannan rajistan amma akwai bukatar a inganta shi hakan yasa ake tattara bayanai a yanzu

Gwamnatin tarayya tana shirin kaddamar da rajista na musamman na kasa don talakawa mazauna Najeriya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar gwamnatin, rajistan zai taimaka mata wurin yunkurin da ta ke yi na tsamo miliyoyin 'yan Najeriya daga kangin talauci domin za ta san ainihin adadin mutanen da ke fama da talauci a kasar.

Gwamnatin ta sha maimaita cewa tana da shiri na tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

A jawabin da tayi na bikin ranar kawar da talauci na kasa da kasa, Ministan ayyukan tallafawa al'umma da ayyukan cigaba, Sadiya Faouq ta ce nan ba da dadewa ba za a fitar da rajista guda dauke da sunayen mutanen da ke fama da talauci.

Ta ce, "Za mu fitar da rajista. Mun san cewa akwai wani rajistan guda daya amma za mu inganta shi. Abinda za mu fara yi shine tattara bayanai domin idan babu bayanai ba za mu iya cimma abinda muka saka a gaba ba. Saboda haka za mu fito da rajista na talakawa guda daya ba da dadewa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel