Kwamishinan yada labarai ya karyata surutan cewa Gwamna Akeredolu bai da lafiya

Kwamishinan yada labarai ya karyata surutan cewa Gwamna Akeredolu bai da lafiya

Rashin ganin Rotimi Akeredolu a ofis cikin ‘yan kwanakin nan ya sa jama’a sun fito su na tofa albarkacin bakinsu inda ta kai har wasu sun fara yada cewa gwamnan yana jinya ne a asibiti.

Jita-jitar da ke yawo kamar yadda mu ka samu labari shi ne ana zargin gwamnan ya ci wani abu ne da ya bata masa ciki. Mataimakin gwamna, Agboola Ajayi, shi ne ke jan ragamar jihar a yanzu.

Sai dai kwamishinan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar Ondo, ya yi wuf ya karyata rade-radin inda ya fayyace cewa Mai girma gwamnan na nan garau da koshin lafiyarsa.

Mista Donald Ojogo ya kuma tabbatar da cewa gwamna Rotimi Akeredolu bai ci wani abu da ya bata masa ciki kamar yadda ake rayawa ba. Wannan zai sa hankalin wasu jama’an ya kwanta.

KU KARANTA: Zan ba Mata rabin kujerun mukamai a mulki na – Gwamnan Ogun

Donald Ojogo ya sanar da ‘yan jarida cewa Rotimi Akeredolu ya tafi hutunsa na shekara ne kuma tuni ya dawo amma ya tsaya a babban birnin tarayya Abuja inda yake kan wasu batutuwan jihar.

Ojogo ya yi wa Manema labarai wannan jawabi ne a Alhamis, 17 ga Watan Oktoba, 2019 lokacin da ya gana da su a Garin Akure. Kwamishinan ya gwamnan ya tafi hutu ne bayan bikin ‘Diyarsa.

Ganin cewa zaben Ondo ya karaso, Kwamishinan ya kuma ce daga dalilan da su ka sa gwamnan ya labe a Abuja shi ne ya na wasu taron siyasa domin bai son ya rika zuwa Garin Abuja kullum.

“Mu na jin rade-radi iri-iri a game da gwamna, amma ina sanar da ku cewa wadannan surutai duk daga wasu mutane ne wadanda ba su son ganin zaman lafiya a wannan jihar.” Inji Donald Ojogo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel