Buhari ya bayar da umurnin yin binciken kwa-kwaf a hukumar NDDC

Buhari ya bayar da umurnin yin binciken kwa-kwaf a hukumar NDDC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a Abuja ya bayar da umurnin a gudanar da binciken kwa-kwaf kan yadda ake gudanar da ayyuka a Hukumar Inganta Yankin Neja-Delta (NDDC).

This Day ta ruwaito cewa shugaban kasar ya bayar da umurnin ne saboda yawan koke da ake gudanarwa kan yadda ayyuka ke tafiya a hukumar daga 2001 zuwa 2019.

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman a kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina cikin wata sanarwa ya ce shugaban kasar ya bayar da umurnin ne yayin da ya tarbi tawagar shugabanni daga jihohi 9 na yankin Neja-Delta karkashin jagorancin Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa.

DUBA WANNAN: An zargi tsohon babban hafsan sojojin Najeriya da daukan nauyin wasu tsagerun matasa a Neja-Delta

A cewarsa, shugaban kasar ya fadawa tawagar cewa irin ayyukan da ake gudanar a yankin Neja Delta a halin yanzu bai yi dai-dai da irin makuden kudaden da ake ware wa hukumar ta NDDC ba.

Adesina ya ce shugaban kasar ya ce, "Ina kokari ina bita kan dokar da ya kafa wadannan hukumomin musamman NDDC. Muna bakatar ganin ayyuka a kasa idan aka yi la'akari da irin kudaden da gwamnatin tarayya ta dade tana kwararawa a NDDC; ya kamata wadanda ke jagorancin wurin suyi bayani.

"Sai anyi bayyani kan ayyukan da aka ce anyi. Ba za ka ce ka kashe biliyoyin naira ba amma idan an ziyarci wurin ba za a ga ayyukan da aka yi ba. Kwararrun da aka dauka suma sai sun nuna cewa sun cancani suyi aikin da ake basu."

Ya kuma ce Shugaba Buhari ya amince cewa gudanar da ayyukan cigaba a yankin Neja Delta yana bukatar makuden kudi idan aka kwatanta da sauran yankunan kasar inda ake da kasa mai kwari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel