Karya ne bana shirin barin APC – Obaseki ya bayyana

Karya ne bana shirin barin APC – Obaseki ya bayyana

- Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya bayyana cewa ba ya shirin barin jam’iyyar All Progressives Congress

- Obasaki ya jaddada matsayarsa ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar magoya bayansa

- Ya ce sai dai masu yi masa bita da kulli su fice su bar masa jam'iyyar

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki a ranar Laraba, ya bayyana cewa ba ya shirin barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Obaseki ya fadi hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar magoya bayansa mai suna Godwin Obaseki Support Group lokacin da suka kawo masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Benin.

An bayyana matsayar gwamnan ne a wani jawabi daga ofishin mai bashi shawara na musamman akan labarai.

“Idan wasu mutane suka fara nuna hallaya mara kyau sannan suna ganin za mu bar masu jam’iyyar; sune za su bar mana jam’iyyar,” inji Obaseki.

Obaseki ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar matasa da masu tasowa, don haka gwamnatinsa ta mayar hankali kan gine-ginen abubuwan more rayuwa da sauya abubuwa.

KU KARANTA KUMA: Zaben Bayelsa: Rundunar yan sanda ta shirya tura jami’ai sama da 30,000

Ya yabi kungiyar akan jajircewarta domin marawa gwamnatinsa baya, inda ya bukaci mambobin kungiyar da su hada kai da sauran kungiyoyi dake da tunani irin nasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel