Yau na fara jin labarin raba ayyukan Gwamnati a Majalisa - Adeyeye

Yau na fara jin labarin raba ayyukan Gwamnati a Majalisa - Adeyeye

An gamu da wata ‘yar takkadama a majalisar dattawan Najeriya a Ranar Alhamis inda Kakakin majalisar ya yi magana da ‘yan jarida a kan zargin handame wasu rabon ayyuka da aka yi.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto dazu nan, ya nuna cewa bai taba jin labarin da ya karade gari a halin yanzu ba, na cewa ‘yan majalisa sun samu kujerun daukar aiki a hukumar FIRS ta kasa.

Sanata Adedayo Clement Adeyeye ya bayyana cewa bai san da batun badakalar daukar aiki ba inda har ya tambayi ‘yan jarida su ba shi labarin abin da yake yawo a gari domin ya samu ta cewa.

Adedayo Adeyeye wanda shi ne shugaban kwamitin yada labarai a majalisa ya ce: “Ya kamata in fada maku hakikanin abin da yake kasa, kuma maganar Allah, ban taba jin wannan magana ba.”

KU KARANTA: Na cikin gidan tsohon wani Gwamnan APC ya cire masa zani a kasuwa

“Akwai bukatar in yi bincike, in tuntubi ‘yan kwamitin, in samu bayanin binciken da su ka yi, sannan kuma in zauna da shugabannin majalisa, daga nan ne sai in iya fitowa in yi maku magana”

Adedayo Clement Adeyeye ya karasa jawabin da cewa: “Yanzu ba zan zo in fadi abin da ba daidai ba” Da aka tambayesa ko yana rufawa Abokan aikin na sa asiri ne, sai ya nuna cewa ba haka ba ne.

‘Dan majalisa ya ce: “Ba haka ba ne. Na fada maku ba na Abuja na wani lokaci. Kai, ina ma so in gana da ‘yan jarida Ranar Talata. Abubuwa sun yi mani yawa, wasu su ke fitar da bayani a madadi na.

Mai magana da yawun majalisar dattawan yace da zarar ya karkare bincikensa, zai sanar da jama’a abin da ya auku. Ba mu da masaniyar ainihin lokacin da Sanatan zai zanta da Manema labaran.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel