Zargin cin hanci: Akwai tambayoyin da zaka amsa, kotu tace wa Lawan

Zargin cin hanci: Akwai tambayoyin da zaka amsa, kotu tace wa Lawan

- Babban kotun tarayya dake Apo, Abuja, ta umarci Farouk Lawan, tsohon dan majalisar wakilai da ya kare kansa

- Ana zarginsa ne da karabar hancin $620,000 daga cikin $3,000,000 da yace zai karba

- Zai karba kudin ne don share sunayen wasu kamfanoni da ake tuhuma da waddaka da kudin tallafin man fetur a 2012

Babban kotun tarayya da ke Apo, Abuja, ta umarci tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan da ya kare kanshi akan zargin cin hanci da ake zargin ya karba na tallafin mai.

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta kai Lawan gaban kotu sakamakon zarginsa da ake da bukatar dala miliyan 3 daga shugaban Zenon Petroleum and Gas Limited a 2012, yayin da Lawan din ke shugabantar kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai akan tallafin man fetur.

KU KARANTA: Wata jami’a ta kori malami tare da janye shaidar digirin digirgir dinsa

An zargi cewa, ya karba $620,000 daga cikin kudin da zummar zai cire sunan kamfanonin Otedola daga jerin kamfanonin da ake tuhuma da amfani da tallafin man fetur din ba ta yadda ya dace ba.

Lawan, wanda yayi dan majalisar wakilai sau hud, ya wakilci mazabar tarayya ta Bagwai da Shanono. Ya bukaci kotun da ta bayyana cewa babu wata shari'a akan zargin nasa saboda babu shaidu gamsassu.

Ozekhome, lauyan masu kara, ya kasa bayyana gamsassun shaidu akan laifin kuma shaidun da ya gabatar sun fada kalamai masu sabani da juna akan kudin da ya karba daga Otedola.

Sannan kuma lauyan wanda ake kara, ya bayyana cewa, faifan bidiyon da masu kara suka gabatar bai da hoto mai kyau har da za a gamsu cewa, ambulan din da Otedola ya mikawa Lawan kudi ne a ciki.

Hakazalika, rashin cafke wanda ake zargin da hukumar jami'an tsaro ta farin kaya da basu yi ba zai iya zama shaida na cewa basu da shaida kwakwara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel