Ministar kudi da kuma tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmad ta ce bashin da Najeriya za ta ciyo daga Bankin duniya na dalar Amurka biliyan 3 za ayi amfani da shi ne domin inganta sashen lantarki.
Zainab ta fadi wannan maganar ne a lokacin da take zantawa da ‘yan jarida a birinin Washington DC na Amurka, inda ta je domin halartar taron IMF.
KU KARANTA:Bidiyo: Shugaban kungiyar kwadago ta NLC yayi karin haske a kan tattaunawarsu da gwamnatin tarayya
Ministar wadda ita ce ke jan tawagar gwamnatin Najeriya a wurin taron ta ce za ta yi magana mai zurfi da hukumar bankin duniyan domin ba su bayanin aikin da za ayi da kudin.
Ta ce, a bisa tsarin gwamnatin tarayya na samar da ingantacciyar wutar lantarki, bashin zai yi amfani ne a bangarori biyu na sashen wutar da suka hada kamfanin samarwa da kuma masu bayar da wutar ga jama’a.
Ministar kudin ta ce: “Akwai kudurin gyaran lantarki da gwamnatin Najeriya ke shirin yi kan kudi tsakanin $2.5bn zuwa $3bn. An shirya gudanar da wannan aikin ne domin magance matsalar lantarki a kasar.
“Zamu yi zama na musamman domin tattaunawa da hukumar bankin duniya game da wannan al’amari na wutar lantarki. Makasudin yin hakan kuwa shi ne domin hukumar bankin su samu gamsuwa a kan abinda muke da niyyar yi da bashin idan an bamu.” Inji ta.
Bugu da kari, Zainab Ahmad ta ce bashin zai kasance gida biyu inda za a soma karbar $1.5bn kafin daga baya a karbi sauran cikon.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa