Kungiyar mambobin PDP a majalisa sun fitar da sunayen alkalai 7 da suke son su jagoranci sauroron shari'ar Atiku da Buhari

Kungiyar mambobin PDP a majalisa sun fitar da sunayen alkalai 7 da suke son su jagoranci sauroron shari'ar Atiku da Buhari

Wata kungiyar mambobin jam'iyyar PDP a majalisar wakilai ta lissafa jerin sunayen manyan alkalai 7 da suke fatan su za a nada domin sauraron daukaka karar kalubalantar nasarar da Buhari ya samu a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Mambobin sun bayar da shawarar cewa kamata ya yi a nada Jastis Ibrahim Tanko, Jastis Rhodes-Vivour, Jastis Mary Odili, Jastis Sylvester Ngwata, Jastis Olukayode Ariwoola, Jastis Musa Mohammed da Jastis Kumai Akaahs a matsayin alkalai 7 da zasu saurara sannan su yanke hukunci a karar da Atiku ya daukaka.

Kungiyar mambobin majalisar ta samu goyon bayan uwar jam'iyyar PDP wajen zargin da ta yi a kan cewa ana neman saba wa ka'ida wajen zaben manyan alkalan kotun koli da ya kamata su saurari karar da Atiku ya daukaka.

DUBA WANNAN: Jakadan Najeriya ya bukaci majalisa ta tsige gwamnan PDP a arewa, ya bayyana dalili

A cikin wani jawabi mai dauke da sa hannun Honarabul Kingsley Chinda (shugaba), Honarabul Chukwuma Onyema (mataimakin shugaba), Honarabul Umar Barde (bulaliya) da Honarabul muraina Ajibola (mataimakin bulaliya), kungiyar mambobin ta ce bisa al'ada, ana nada manyan alkalan kotun koli ne domin sauraron daukaka karar kalubalantar zaben shugaban kasa.

Kungiyar ta ce haka aka saba yi tun daga shekarar 1979 tare da yin kira ga kotun koli da alkalin alkalai na kasa a kan su bi doka, su kuma guji duk wani abu da kan iya zama ya ci karo da tanadin doka ko kundin tsarin mulkin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel