Wani kwamishina ya kara barin aiki, ya fadi dalili

Wani kwamishina ya kara barin aiki, ya fadi dalili

- Kwamishinan ma'adani da labarkatun kasa na jihar Bayelsa ya sauka daga kujerarsa

- A wasikar da ya mikawa gwamnan jihar, ya bayyana godiyarsa akan damar da ya bashi na aiki a karkashin gwamnatinsa

- Ya bayyana cewa, ya 'gaji' da aikin ne a don haka ne yake bukatar ya huta tare da bautawa ubangiji da kuma mutane

Kwamishinan ma'adanai na jihar Bayelsa, Markson Fafegha, ya daukaka daga kujerarsa ganin gabatowar zaben 16 ga watan Nuwamba.

Fefegha, sanannen dan siyasa ne a Yenagoa kuma yana daya daga cikin wadanda suka kirkiro gwamnatin Dickson.

Dan siyasar ya bayyana cewa ya gaji da gwamnatin duk da yayi kwamishinan ilimi da kuma babban sakatare Dickson.

A wasikar barin aikin, Fefegha ya yi godiya ga Dickson da ya bashi matsayi kala-kala a gwamnatin.

KU KARANTA: Gaskiyar lamarin: Yadda mijina ya mutu, Maryam Sanda ta sanar da kotu

Ya ce: "Amma bama rayuwa yadda muke so kuma komai na iya canzawa. Bayan dogon nazari, na yanke hukuncin barin mukamina sakamakon rashin tabbas na siyasa da sauran dalilai da na barwa kaina."

"Ina fatan sadaukar da rayuwata da karfina ga sauran aiyukan da zasu sa ubangiji da mutane farinciki da ni. Ina ma gwamnatin fatan alheri da kuma jam'iyyar PDP".

Yayin yanko aya daga littafi mai tsarki, Fefegha ya kara da: "Akwai dalilin komai da ka gani a duniya. Kuma komai kaga ya faru a rayuwarmu, yayi daidai da tsarin Ubangiji".

Bayan haka, mai bada shawara na musamman ga Dickson akan sasanta rikicin man fetur da iskar gas tsakanin jama'a, Chief Tiwe Oruminighe, ya mika wasikar barin aikinsa.

Oruminghe, wanda tsohon shugaba ne a jam'iyyar APC a jihar ya koma PDP bayan da aka kasa sasanta banbance-banbance tsakaninsa da shugaban jam'iyyar APC na jihar, Chief Timipre Sylva.

Amma Oruminighe, wanda ya kammala shawarar komawa jam'iyyar APC, ya sanar da Dickson cewa shi dai saboda rashin zaman lafiyar da ke tunkarowa ne a zaben jihar na 2019 zai sa ya koma tsohuwar jam'iyyarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel