Zaben Bayelsa: Rundunar yan sanda ta shirya tura jami’ai sama da 30,000

Zaben Bayelsa: Rundunar yan sanda ta shirya tura jami’ai sama da 30,000

- Sufeto janar na yan sanda ya sha alwashin cewa za a samar da isasshen tsaro don zaben watan Nuwamba a jihar Bayelsa

- Shugaban yan sandan yace za a tura jami’an tsaro sama da 30,000 daga hukumomin tsaro daban daban zuwa jihar gabannin zaben

- A cewar IGP, rundunar yan sanda zata tabbatar da fagen wasa ga jam’iyyun siyasa da yan siyasa

Rundunar yan sandan Najeriya tace za ta tura jami'ai sama da 30,000 a zaben gwamna na watan Nuwamban 2019 mai zuwa a jihar Bayelsa.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa sufeto janar a yan sanda, Mohammed Adamu, yayinda yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a Yenagoa yace jami'an za su hada da jami'ai daga sauran hukumomin tsaro.

Adamu wanda ya samu wakilcin mataimakin sufet janar na yan sanda (ayyuka), Abdulmajid Ali, yace yan sandan ba za su ba kowani dan siyasa ko jam'iyya damar yin yadda ya ga dama ba.

Yace jami’an tsaron da za’a tura don zaben har ila yau za su samar da fagen wasa don tabbatar da zaben gaskiya da adalci.

Har ila yau ya bayyana cewa za a hukunta duk wani wanda ya keta doka ko janyo barazana ga kwanciyar hankali yayin gudanar da zabe.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta mika godiya ga mijinta akan nada mata sabbin hadimai

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a bayacewa wani shugaban gargajiya a daular Ekpetiama dake jihar Bayelsa yayi zargin cewa wassu ya mn siyasa suna shirya makamai don haddasa tashin hankali a zaben Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel