Karar Kwana: Zazzafan fate ya salwantar da rayukan kananan yara 3 a Bauchi

Karar Kwana: Zazzafan fate ya salwantar da rayukan kananan yara 3 a Bauchi

Hakika mutuwa riga ce ta kowa wadda ba ta fita kuma muddin ajali yayi kira sai an amsa, hakan ya sanya wani mummunan tsautsayi ya yi sanadiyar salwantar rayukan kananan yara uku yayin da fate mai tsananin zafi ya kwaranya jikinsu.

Ajali ya katse hanzarin yaran uku ne 'yan tsakanin watanni 9 zuwa shekaru 9, yayin da wani zazzafan fate ya kwaranya a jikinsu cikin wani baburin Adaidatu Sahu a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, tsautsayin ya auku ne yayin da aka dauko faten cikin wani babban tulun zamani mai rike zafin abinci a baburin mai kafafu uku, wanda yunkurin kaucewa wani rami ya haddasa tangal-tangal ta kwaranyar zazzafan faten a kan mutanen da ke cikin sa.

Da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, wani dan uwan wadanda tsautsayin ya afka wa, Mallam Auwa Bala, ya ce mummunan tsautsayin ya auku a ranar Larabar makon da ya shude yayin da ake tsaka da shagalin biki daya daga cikin 'yan dangi.

"Mata uku da kananan yara sun kasance cikin baburin mai kafafu uku wanda ya dauko zazzafan faten, wani nau'in abincin gargajiya da wasu ke kira 'gwate', da za'a garzaya da shi domin sharba a wurin shagalin biki."

"Tsautsayi ya sanya tulu mai dauke da zazzafan faten ya kife tare da kwaranya a wasu sassan jiki na kananan yaran da suka hadar da kai, kirji da kuma kafadunsu."

"Yara uku da suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da Aniya Yahaya mai shekaru 6, Mariam Muhammad mai shekaru 9 da kuma Ibrahim Yusuf dan watanni tara wadanda zafin kuna ya sanya suka ce ga garin ku nan. Haka kuma akwai Khadija Usman mai shekaru 7 wadda a haliin yanzu tana nan rai a hannun Mai Duka," inji Malam Bala.

KARANTA KUMA: Ba kamfanonin sadarwa kadai ne ke sace wa 'yan Najeriya data ba - NCC

Ya ce daya daga cikin matan ta samu raunuka da dama yayin da sauran kananan yaran biyu suka tsallake rijiya da baya babu ko kwarzane.

Ya kara da cewa, mutuwar 'yan dangi uku a lokaci guda babban rashi ne, sai dai babu yadda suka iya face su dauki dangana tare da rungumar kaddara domin kuwa Mai Duka da ya bayar da su shi ne kuma ya karbe abinsa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel