Ba kamfanonin sadarwa kadai ne ke sace wa 'yan Najeriya data ba - NCC

Ba kamfanonin sadarwa kadai ne ke sace wa 'yan Najeriya data ba - NCC

Hukumar NCC mai kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya, ta hikaito wasu hanyoyi na daban masu tarin yawa wanda tsarin bayar da 'yancin shiga yanar gizo wato 'data' a wayoyin salula ke saurin karewa ba tare da an farga ba.

A yayin hikaito wannan hanyoyi sabanin yadda mafi akasarin al'ummar kasar nan ke ikirari, hukumar NCC ta ce kada a koda yaushe a rinka zargin kamfanonin sadarwa na layukan waya da laifin zirarewar data ba gaira ba dalili.

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, da yawa daga cikin al'ummar Najeriya na zargin kamfanonin layukan waya da laifin yashe masu data cikin gaggawa yayin da suka shiga wasu ganin rahotannin duniya a yanar gizo.

Hukumar ta ce "ba ko yaushe bane kamfanonin waya ke da laifin karar da data ba gaira ba dalili, idan masu amfani da intanet a waya suka ga data a wayarsu na saurin karewa".

A sanadiyar haka hukumar NCC ta kirkiri layin 622 na yin kira kyauta babu ko sisi domin shigar da korafi a duk sa'ilin da wani kamfanin sadarwa ya yashe wa wani data ba da bai tabbatar da dalilin hakan ba.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin shugaban hukumar NCC na kasa, Farfesa Umar Danbatta, yayin wata ganawa da ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami da kuma wasu manyan jami'ai na ma'aikatar.

KARANTA KUMA: An fidda sunayen gwarazan 'yan kwallo 100 a karni na 21

Farfesa Danbatta ya bayyana cewa, an gano hakan ne a sanadiyar bunkasar ilimin kimiyya da ya janyo wasu manhajoji daban-daban da ak kirkira musamman domin wayoyin salula na zamani na sabunta kansu ba tare da mai wayar ya farga ba, lamarin da ya sanya data sai ta rinka zirarewa ba tare da an ankara ba.

Haka kuma ya ce akwai wasu shafukan yanar gizo masu yawan nuna tallace-tallace ta hanyar amfani da hoto ko kuma bidiyo wanda a mafi yawancin lokaci sukan bude kansu ba tare da mutum ya ankara ba, da a sanadiyar haka data ke saurin karewa.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar NCC ta ce za ta kara bita ko kuma waiwayar batun farashin siyan data da kuma ingancinta.

A nasa jawabin, ministan ya nemi hukumar NCC da ta gaggauta wayar da kan al'ummar Najeriya a zaurukan sada zumunta ta hanyar amfani da harsuna daban-daban domin ankarar da su a kan gaskiyar lamarin.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel