Jami'an tsaro sun tarwatsa gangamin 'yan shi'a a Abuja

Jami'an tsaro sun tarwatsa gangamin 'yan shi'a a Abuja

Muryar Duniya ta ruwaito cewa, mambobin kungiyar IMN wadda aka fi sani da Shi'a Najeriya, a ranar Juma'a sun fara aiwatar da gangamin sharar fage na tattakin da suka kudirci yi a ranar Asabar, domin tunawa da bakin cikin ranar Arba'een, wato tuna wa da zagayowar ranar Arba'in ta zaman mamkokin kisan gillar da aka yi wa Imam Hussein.

Jim kadan bayan soma tattakin a ranar Juma'ar da ta gabata, jami'an tsaro na hukumar 'yan sanda suka fatattaki gangamin ta hanyar harbi cikin iska da kuma amfani da 'Tear Gas' wato hayaki mai sanya hawaye wanda wasu ke kira Barkonon Tsohuwa.

Babu shakka gwamnatin Najeriya da kuma rundunar 'yan sandan kasar bisa ga hukunci na shari'a, sun sha nanata hukuncin kaddamar da haramci a kan dukkanin wata gudanarwa da 'yan shi'a za su yi a kasar nan.

A watannin baya ne dai gwamnatin Najeriya ta haramta ayyukan mabiya shi'a, sanadiyar arangamar da rinka aukuwa a lokuta mabanbanta tsakaninsu da jami'an tsaro, tun bayan tsare jagoransu, Shiekh Ibrahim El-Zakzaky da kuma mai dakinsa, Zeenatu, wanda hukumar 'yan sandan farin kaya DSS tayi a watan Dasumban 2015.

A rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, tun a makon da ya gabata ne mambobin kungiyar Shi'a a Najeriya, suka bayyana aniyyarsu ta gudanar da tattakin nan na Arba'een a ranar Asabar wanda suka saba a kowace shekara.

Kamar dai sauran takwarorinsu na duniya, mabiya shi'a a Najeriya za su yi tattakin Arbaeen wato tuna wa da kisan jikan Manzon Tsira, Imam Hussain, a shekara ta 61 bayan hijira.

Kungiyar Shi'a na kuma gudanar da tattakin na Arbaeen dangane da ikirarin yadda aka daure wasu daga cikin 'yan uwan Manzo da sarka kuma aka rinka jansu a kar tun daga garin Karbala na kasar Iraqi har zuwa Damashka na Syria.

KARANTA KUMA: EFCC ta cafke 'yan damfara 9 a Enugu

Sai dai kungiyar ta tabbatar wa da al'ummar kasar nan cewa, za ta gudanar da tattakin nata cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da cuzguni ko kuma dakile hakkin kowane bil Adama ta kowace siga.

A rahoton da jaridar The Nation ta ruwaito, kungiyar yayin shan alwashi ta bayar da tabbaci, ta yi kira ga dukkanin al'ummar kasar a kan kada su tayar da hankulansu domin kuwa tattakin na Arbaeen ba zai kawo wata tangarda ba.

Furucin kungiyar ya zo ne a ranar Alhamis cikin wata sanarwa da kakakinta na kasa, Ibrahim Musa, ya gabatar. Ya ce akwai yiwuwar hukumomin tsaron kasar nan su kai musu hari yayin tattakin kamar yadda ta kasance a bara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel