EFCC ta cafke 'yan damfara 9 a Enugu

EFCC ta cafke 'yan damfara 9 a Enugu

Babu shakka ruwa ya kare wa 'dan Kada a yayin da hukumar nan ta EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a reshenta na jihar Enugu, ta samu nasarar cafke wasu madamfaran yanar gizo 9 da suka hadar har da mace a ranar Juma'a.

Biyo bayan wani simame da jami'an hukumar EFCC suka kai a ranar Juma'ar da ta gabata cikin wani gida mai sunan Mexmemphis Properties and Apartments da ke unguwar Maryland, sun samu nasarar cafke ababen zargin 9 kamar yadda kafar watsa labarai ta PM News ta ruwaito.

Mazambatan tara da suka shiga hannu a ranar 18 ga watan Oktoba cikin birnin Enugu sun hadar da; Precious Ibegbulem, Michael Odishi, Ebuka Kenneth, Akabuke Beluolisa, Chibueze Ezeagwu, Nnamdi Maduekwe, Kingsley Orazulike da Uche Nwosu. Sai kuma macen guda cikon ta tara mai sunan Linda Chidera.

An tattaro cewa, hukumar EFCC ta kai simamen ne bayan wani binciken leken asiri da ta gudanar wanda ya tabbatar da irin rayuwa ta rashin gaskiya da matasan ke yi.

KARANTA KUMA: Manyan Bankuna 6 da suka fi samun riba a Najeriya

Sauran ababen da hukumar EFCC ta samu a hannun masu laifin sun hadar da wayoyin salula dama, na'urorin kwamfuta mai tafi da gidanka, motoci na alfarma samfurin Toyota Corolla masu dauke da lambobin DM 722 YAB da LSR 468 FW.

A yayin da hukumar EFCC ta dukufa wajen gudanar da bincike, ta ce za ta gurfanar da ababen zargin a gaban Kuliya inda kowannensu zai fuskanci hukunci kwatankwancin laifin da ya aikata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel