Bidiyo: Shugaban kungiyar kwadago ta NLC yayi karin haske a kan tattaunawarsu da gwamnatin tarayya

Bidiyo: Shugaban kungiyar kwadago ta NLC yayi karin haske a kan tattaunawarsu da gwamnatin tarayya

Bayan tsawon awa 7 ana ganawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyi kwadago a kan kaddamar da sabon mafi karancin albashi. Shugaban kungiyar kwadago ta NLC yayi karin haske a cikin wani bidiyo game da zaman.

Tun ranar Talata aka soma zaman wanda ba a kammala shi ba har zuwa lokacin da muke kawo maku wannan rahoton.

KU KARANTA:Masu garkuwa da mutane sun sako mutum 6 a Abuja bayan an biya su miliyan N6

An fara zaman ne a na ranar Laraba da misalin karfe 5 na yamma wanda ya kai har karfe 2:15 na ranar Alhamis 17 ga watan Oktoba.

A halin yanzu dai bangarorin biyu sun aminta da dage zaman har zuwa karfe 7 na yammacin Alhamis.

Ga abinda Ayuba Wabba yake fadi game da tattaunawarsu da gwamnatin tarayya a cikin wannan bidiyon.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel