Wani minista ya rasa ransa bayan ya fado daga bene mai hawa 8

Wani minista ya rasa ransa bayan ya fado daga bene mai hawa 8

- A yau Alhamis ne mataimakin ministan ilimi na kasar Vietnam ya sullubo daga bene mai hawa 8

- A take kuwa ya rasa ransa, abinda ya kawo zargi da cece-kuce a kafafen sada zumunta

- A halin yanzu dai 'yan sanda na tattara bayanai tare da binciken silar mutuwar

A ranar Alhamis ne mataimakin ministan ilimin Vietnam ya rasu sakamakon fadowa da yayi daga ofishinsa da ke bene hawa na takwas, in ji ma'aikatar.

Le Hai An, mai shekaru 48 a duniya ya rasu ne da misalin karfe 7:10 na safiyar ranar Alhamis.

Ma'aikatar ilimin ta ruwaito cewa hatsari ne duk da ba a gano sanadin hakan ba.

KU KARANTA: Gaskiyar lamarin: Yadda mijina ya mutu, Maryam Sanda ta sanar da kotu

Kamar yadda jaridar Dan Tri ta kasar Vietnam ta ruwaito, An ya fado ne daga barandar da ke wajen cin abincin ma'aikatar.

'Yan sanda na duba wajen da abin ya faru don hada gamsasshen bayani game da abinda ya auku.

Mutuwarsa ta farat daya ta sanya hasashe tare da zargi a kafafen sada zumunta.

An, zai halarci wani taro na ma'aikatar ilimin ta kasar a ranar Alhamis din wacce minitsan ilimi, Phung Xuan Nha ai jagoranta.

An zabeshi ne a shekarar 2018 yayin da yake shugaban jami'ar hakar ma'adanai ta Hanoi. Akwai sa ran An ne zai zama ministan ilimi na kasar a shekarar 2021.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel