An gurfanar da iyaye kan aurar da diyarsu mai ciki ga wani saurayi a Kaduna

An gurfanar da iyaye kan aurar da diyarsu mai ciki ga wani saurayi a Kaduna

Wani matashi dan shekara 35 mai suna Ibrahim Adamu ya gurfanar da surukansa, iyayen matarsa gaban wata kotun shari’ar musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari, cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa kan zarginsu da yaudararsa.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito Ibrahim yana tuhumar surukan nasa ne da laifin caka masa diyarsu wanda ya aura, sakamakon zarginsu da yake cewa suna da masaniyar tana dauke da cikin shege, amma suka aura masa ita.

KU KARANTA: Dubun wani gagararren mai garkuwa da mutane ta cika, Yansanda sun halaka shi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito iyayen yarinyar sun hada da Sani Dogon-Zikiri da Laura Sani, wadanda matashin yake tuhumarsu da laifin cin amana da kuma yaudara.

Ibrahim, wanda mazaunin kauyen Rijana ne ya shaida ma kotun cewa matarsa Nafisa ta hada baki da iyayenta wajen aurar da ita gareshi, alhali kuwa dukkaninsu suna sane da cikin da take dauke da shi.

Lauyan Ibrahim yace: “Wanda ake kara tare da matarsa sun tafi wajen gwajin ciki jim kadan bayan aurensu, inda aka tabbatar da tana dauke da juna biyu, cikin daya kai makonni biyu tun kafin su yi aure. Daga nan ya tambayi matarsa labarin cikin, kuma ta tabbatar masa da cewa ba cikinsa bane.”

Don haka lauyan ya nemi kotu ta umarci surukan Ibrahim su biyashi zunzurutun kudi N100,000 saboda yaudararsa da suka yi, amma surukan ta bakin lauyansu, Abubakar Suleiman sun musanta tuhume tuhumen.

Dalilinsu kuwa shine kamata ya yi Ibrahim ya bayyana musu halin da ake ciki tun a lokacin daya gano cikin shegen, ba wai sai yanzu da matar ta haihu ba, don haka suka ce wannan ya nuna cewa jaririn da aka haifa yaron Ibrahim ne, don haka babu bukatar biyansa ko sisi.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkali mai shari Muhammad Adamu-Shehu ya dage karar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba domin baiwa mai kara daman kawo shaidunsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel