An zargi tsohon babban hafsan sojojin Najeriya da daukan nauyin wasu tsagerun matasa a Neja-Delta

An zargi tsohon babban hafsan sojojin Najeriya da daukan nauyin wasu tsagerun matasa a Neja-Delta

A yayin da rikici ke kara kazanta a garin Uzere na karamar hukumar Isoko ta jihar Delta, ana zargin cewa matasa masu tayar da kayan baya na Neja Delta suna samun mafaka ne a gidan tsohon shugaban hafsin sojojin kasa, Janar Alexander Ogomudia (ritaya).

Mazauna garin da suke tsere daga gidajensu sun shaidawa Sahara Reporters a ranar Laraba cewa matasan da ke kiran kansu masu 'fafutikan neman 'yanci' suna zaune ne a gidan Ogumudia da ake yi wa kalon daya daga cikin mai daukan nauyinsu.

Wani malamin makarantar sakandire da ya nemi a boye sunansa ya ce, "Fiye da kashi 40 na matasan masu da suka dauki makamai yaran Sam Ogri ne yayin da kuma sauran yaran Janar Ogomudia ne. An ce David, hadimin dan majalisar jiha mai wakiltan mazabar Isoko ta Kudu II a majalisar jihar yana daya daga cikin matasan da ke fitinar mutanen garin."

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Wasu mazauna garin sun zargi shugaban kungiyar Isoko, Iduh Amadhe a matsayin wanda ya tayar da rikicin don ya mayar da tsohon basaraken da aka tsige mai suna Odogri kan mulkinsa amma wasu mutane ciki har da Ogomudia sun ki amincewa.

Rahotanni sun ce matasan da ke kiran kansu 'masu neman 'yanci' ne suka juya garin duk da cewa akwai jami'an tsaro da aka tura domin kwantar da tarzomar.

A martanin da ya yi kan zargin da ake masa, Ogomudia ya ce shugaban karamar hukumar Isoko ta Kudu, Itiako Ikpokpo ne ya janyo rikicin da ke faruwa a garin, ya ce: "Ni ina zaune a Legas ne, rikicin kuma a can ake yi. Ta yaya za a ce ina samarwa matasa makamai kuma ina basu mafaka a gida na? Wasu mutanen banza ne da ke kokarin bata min suna. Na shiga soja har na zama babba kuma na yi wa kasa ta hidima da kyau."

Janar Ogomudia ya kara da cewa wadanda ke zarginsa da hannu cikin rikicin suna bakin ciki ne saboda irin matsayin da Allah ya taimake shi ya kai a kasar nan kuma ya ce ba zai bari kowa ya shafa masa 'kashin kaza ba'.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel