Rage albashi: Ma'aikatan NASS sun shiga fargaba

Rage albashi: Ma'aikatan NASS sun shiga fargaba

- Fargaba a yau ta shiga zukatan 'yan majalisar tarayya sakamakon zabge albashin mataimakansu na musamman da majalisar ta yi

- A tsakanin watan Yuni da Augusta ne mataimakan na musamman aka basu wasikun dauka aikin

- Ana zaton majalisar tayi hakan ne don samun damar biyan karancin albashin ma'aikata

Majalisar dattawa ta zaftare albashi tare da alawus din sama da mataimaka 3,000 na ‘yan majalisar.

Mataimakan da sanatoci 109 da ‘yan majalisar wakilai 360 suka dauka aiki sun fara samun wasikun daukar aikin ne a watan Yuni, 2019 inda wasu kuma suke tsammatar tasu.

KU KARANTA: Ko sau nawa zamu tsaya gaban alkali, mu ke da nasara, in ji ‘yan shi’a

A binciken da wakilin jaridar The Nation ya gudanar, mataimakan sun samu wasikar daukarsu aikin ne a tsakanin watan Yuni da Augusta amma yanzu an bukacesu da su dawo dasu don karbar sabbin wasikun daukar aikin.

A sabbin wasikun, akwai zabge albashinsu da aka yin a kusan N500,000 zuwa N1,000,000 a cikin jimillar albashin shekara daya.

A misali, mataimakin dan majalisa na musamman da aka dauka a matsayi na 13, waccan wasikarsa na dauke da albashin N3.3m a shekara daya. Sabuwar wasikar kuma na kunshe da N2.6m wanda ke nuna zabgewar wajen dubu dari bakwai a tsohon albashin.

Ana tsammanin cewa, kokarin cika alkawarin karancin albashin ma’aikatan Najeriya ne ya jawo zabge albashin mataimakan ‘yan majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel