Aisha Buhari ta mika godiya ga mijinta akan nada mata sabbin hadimai

Aisha Buhari ta mika godiya ga mijinta akan nada mata sabbin hadimai

Uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari, ta mika godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan amincewa da nadin hadimiai shida a ofishinta.

Misis Buhari ta nuna jin dadinta a ranar Laraba, 16 ga watan OPktoba, lokacin da ta karbi bakuncin matan gwamnoni da suka kai mata ziyara a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Wadanda aka nada sune Dakta Mairo Almakura, Mai taimakawa ta musamman kan African First Ladies Mission (AFLPM); Muhammad Albishir, Mai taimakawa na musamman kan Kungiyar Cigaba da First Ladies na kasashen Afirka (OAFLD).

Sauran sune; Wole Aboderin, Mai taimakawa na musamman kan kungiyoyin masu zaman kansu (NGOs); Barrista Aliyu Abdullahi, Mai taimakawa ta musamman kan Kafafen watsa labarai; Zainab Kazeem, Mai taimakawa ta musamman kan Harkokin cikin gida da taruka; Funke Adesiyan; Mai taimakawa ta kusa Harkoki cikin gida da taruka.

KU KARANTA KUMA: Shugabannin Igbo sun nemi a hukunta wadanda suka sace yara 9 a Kano

Nadin nasu ya fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Dr Aisha Muhammadu Buhari a ranar Laraba 16 ga watan Oktoba, 2019 ta fadi cewa za ta gina sakatariya wa Kungiyar matan shugabannin Afirka wadda aka fi sani da African First Ladies Peace Mission (AFLPM).

A shekarar 1995 ne aka kafa wannan kungiyar a karo na farko a birnin Beijing dake kasar China, tun daga lokacin har zuwa yanzu kungiyar na karkashin kulawar Najeriya ne, inda matan shugabannin kasashen Afirka ke musayar jan ragamarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel