Mata 2, Maza bakwai: Kotun Kaduna ta saki mabiya Shi'a 9 bayan shekara uku

Mata 2, Maza bakwai: Kotun Kaduna ta saki mabiya Shi'a 9 bayan shekara uku

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Kaduna ta saki mabiya kungiyar Shi'a 9 da aka kama bayan gwamnati ta haramta harkokin kungiyar Shi'a (IMN) da ke karkashin shugabancin Sheikh El-Zakzaky.

An saki mambobin kungiyar 9 da suka hada da mata biyu, bayan an kama su a shekarar 2016, shekaru uku da suka wuce, yayin da suka fito domin gudanar da tattakin Ashura a garin Kaduna.

A cewar jawabin da kakakin kungiyar IMN, Ibrahim Musa, ya fitar, ya ce alkalin kotun, Jastis Shiri Nyom, ya sallami mambobin kungiyar bayan ya wanke su daga dukkan tuhumar da ake yi musu.

A cewar jawabin kakakin, Jastis Nyoms, ya ce masu kara sun kasa tabbatar wa kotun da laifun mambobin 9 da aka gurfanar.

DUBA WANNAN: FG ta kori mambobin jam'iyyar DPRK 7, ta haramta musu dawowa Najeriya har abada

Kungiyar IMN ta ce sakin mambobinta 9 ya kara shiga sahun nasarorin da kungiyar ke cigaba da samu a kotuna a kan gwamnati tun bayan kisan kiyashin magoya bayanta a Zaria a shekarar 2015.

Sanarwar ta kara da cewa, ya zuwa yanzu an saki daruruwan mambobim kungiyar IMN da aka kama tare da wanke su daga zargin da ake yi musu a gaban kotunan da aka gurfanar da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel