Dubun wani gagararren mai garkuwa da mutane ta cika, Yansanda sun halaka shi

Dubun wani gagararren mai garkuwa da mutane ta cika, Yansanda sun halaka shi

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya, reshen jahar Ribas Fatakwal sun samu nasarar halaka wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da ake kira da suna Agabiseigbe, inji rahoton jaridar Blue Print.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito barawon ya yi kaurin suna wajen tare babbar hanyar Owerri zuwa Fatakwal inda yake sace mutane, tare da yin garkuwa dasu har sai an biyashi kudin fansa, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar, DSP Nnamdi Omoni ya tabbatar.

KU KARANTA: Ku dage da addu’a don shawo kan matsalolin Najeriya - Ahmad Lawan ga yan Najeriya

DSP Omoni yace Yansanda sun kashe barawon ne a karamar hukumar Ikwerre ta jahar Ribas a yayin da yake kokarin kama wasu fasinjojin motar haya tare da yaransa, wanda hakan ya janyo musayar wuta a tsakaninsu.

“A lokacin da miyagun suka hangi dakarun Yansanda, sai suka bude mana wuta, nan da nan jami’anmu suka mayar musu da wuta, a sanadiyyar haka muka kashe jagoransu, muka jikkata wani daban, sa’annan sauran suka tsere dauke da rauni a jikkunansu.” Inji shi.

Daga karshe DSP ya yi kira ga jama’a dasu basu bayani a kan duk wani mutumin da suka gani yana neman a dubashi a asibiti idan har ciwon yayi kama da raunin harsashi, sa’annan yace sun kwace bindigar AK 47 guda daya da alburusai da dama.

A wani labarin kuma, Wasu gungun matasa yan bangan siyasa sun tayar da rikici a yayin da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ke ganawa da jam’iyyun siyasa a jahar Bayelsa inda ake tattauna shirin da hukumar ke yi gabanin zaben gwamnan jahar dake karatowa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel