Karancin albashi: An tashi baram baram tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago

Karancin albashi: An tashi baram baram tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago

An tashi baram baram a tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da shuwagabannin kungiyar kwadago ta Najeriya, ba tare da cimma wata tamaimiyar matsaya ba, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe 5 na yammacin laraba aka shiga tattaunawar inda aka kai har zuwa tsakar dare ba tare da cimma wata matsaya ba, bangarorin biyu sun gagara samun daidaito a kan batun gyaran albashin ma’aikata a sanadiyyar karancin albashin N30,000.

KU KARANTA: Ku dage da addu’a don shawo kan matsalolin Najeriya - Ahmad Lawan ga yan Najeriya

Daga karshe bangarorin biyu sun amince za’a cigaba da zama da misalin karfe 7 na yammacin Alhamis, 17 ga watan Oktoba. A karshen zaman, ministan kwadago, Chris Ngige ya bayyana ma manema labaru cewa an baiwa wasu kwamitocin aikin da ake sa ran zasu kammala kafin a cimma matsaya a tattaunawar.

“Mun samu nasarori, amma dai bamu kai ga cimma yarjejeniya ba, akwai lisaffe lissafen da muke bukatar wasu kwamitoci su kawo mana, kun dai gani har tsakar dare muka kai, mun yi haka ne da kyakkyar niyya don ganin mun karkare tattaunawar.” Inji Minista.

Shi ma shugaban kungiyar kwadago, Ayuba Wabba ya bayyana cewa zasu bayyana ma yan Najeriya halin da ake ciki da zarar an kammala zaman da za’a cigaba a ranar Alhamis.

Idan za’a tuna kungiyar kwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki a makon data gabata idan har gwamnati bata amsa bukatunsu ba zuwa ranar Laraba, hakan tasa gwamnati ta gayyaci kungiyar teburin tattaunawa a ranar Talata don lalubo bakin zaren.

Takaddamar da ta rage a yanzu itace kashi nawa za’a yi ma ma’aikata karin albashi? Yayin da kungiyar kwadago ke neman karin kashi 29 ga ma’aikatan dake tsakanin mataki na 07 zuwa 14, kashi 24 ga ma’aikatan mataki na 15 zuwa 17, ita kuwa gwamnati ta nemi a kara kashi 11 ga ma’aikatan mataki 07-14, da kashi 6.5 ga ma’aikatan mataki na 15-17.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel