Masu garkuwa da mutane sun sako mutum 6 a Abuja bayan an biya su miliyan N6

Masu garkuwa da mutane sun sako mutum 6 a Abuja bayan an biya su miliyan N6

Rundunar ‘yan sandan Abuja a jiya Laraba 16 ga watan Oktoba, 2019 ta bayar da tabbacin ceto mutum 6 daga cikin mutane 10 da wadansu ‘yan bindiga suka sace a garin Kuje cikin makon da ya gabata.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Anjuguri Manzahp, ya ce, jami’an ‘yan sanda tare da sauran hukumomin tsaro na cigaba da yin kokarin ganin cewa an ceto dukkanin wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.

KU KARANTA:‘Yan kasuwa sun yi biris da umarnin NAFDAC, sun cigaba da sayar da Sniper

Ya kara da cewa, jami’an tsaro na yin aiki ba dare da ba rana domin ganin sun ceto wadanda aka sace. Haka kuma yayi kira ga al’ummar Abuja da su kwantar da hankalinsu game da wannan matsalar kana kuma su sana da ‘yan sanda duk wani labarin da suka sani zai taimaka masu.

Manzahp ya ce: “Ba za muyi kasa a gwiwa ba har sai mun ga bayan masu tayar da zaune tsaye tare da hana mutane zaman lafiya a wannan gari.

“Muna cigaba da shirin sanya hannun masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban na Abuja domin magance wannan matsala. Samar da zaman lafiya a ko wane lokaci shi ne burinmu.” Inji shi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito mana cewa, kafin a sako mutum shidan said a aka biya naira miliyan 6 a matsayin fansa. Mai garin Pegi ne ya tabbatar da wannan labarin cewa lallai an biya kudi fansa kafin a sako mutanen kuma cikinsu har da yara kanana.

Mista Irimiah Sarki ya ce: “Iyalan wadannan mutanen su zo har fadata sun sanar da ni kudin da suka biya, daga masu miliyan N3, miliyan N2, miliyan N1 har da masu naira 800,000 akwai, dangane da yadda kuka yi ciniki da barayin.”

https://www.vanguardngr.com/2019/10/kidnappers-free-six-victims-in-abuja-after-collecting-n6m-ransom/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel