Dalilai biyu ne suka sa na yi murabus daga taka leda a kungiyar kwallon kafa ta kasa - Mikel Obi

Dalilai biyu ne suka sa na yi murabus daga taka leda a kungiyar kwallon kafa ta kasa - Mikel Obi

Tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa (Super Eagles), John Mikel Obi, ya bayyana daliali biyu da suka sa ya yi murabus daga taka leda a Najeriya jimmkadan bayan kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka yi a kasar Misra (Egypt).

Obi ya bayyana cewa dalili na farko da yasa shi yin murabus shine domin ya bawa matasan 'yan wasa masu taso wa wuri bayan ya shafe kusan shekaru 20 yana hidimtawa kungiyar 'Super Eagles', kuma a cewarsa, lokacin da zai daina buga kwallo gaba daya yana kara matso wa.

Duk da ya bayyana cewa burinsa ya kasance cikin masu horar wa a kungiyar Chelsea, Obi ya bayyana cewa yana da karfin gwuiwar cewa tauraruwar kungiyar 'Super Eagles' za ta cigaba da haska wa saboda hazikai kuma jajirtattun 'yan wasa.

Obi, tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta 'Chelsea' da ke kasar Ingila, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar 'Trabzonspor'.

DUBA WANNAN: Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 351 a jihohin arewa uku - FRSC

Dalili na biyu da dan wasan ya bayar shine domin ya mayar da hankalinsa gaba daya a kan sabuwar kungiyarsa, Middlesbrough.

"Yanzu haka muna da 'yan wasa hazikai kuma matasa. Suna da basira sosai. Ina da kyakyawan zaton cewa zasu iya fuskantar kalubalen da ke gaban kungiyar 'Super Eagles'. Akwai bukatar na bawa wadannan matasa dama, bayan haka, bani da shekaru masu yawa a gabana a cikin harkar kwallon kafa. Ina son na tattara hankalina a kan kungiya ta a sauran lokacin da ya rage min," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel