Kuma dai! An sake garkuwa da mutane 4 a Abuja

Kuma dai! An sake garkuwa da mutane 4 a Abuja

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mutane biyu a garin Abaji, babbar birnin tarayya Abuja.

An sace Murtala Maji Nasara da Yusuf Ibrahim ne cikin daren Laraba misalin karfe 1 yayinda yan bindigan suka dira garin.

Wani makwabcin daya daga cikin mutanen da aka sace mai suna Yahaya, ya ce yan bindigan yan bindigan sun shigo garin ne ta cikin daji kuma suka fara shiga gidan Murtala Maji.

Ya ce yayinda wani sashen yan bindigan suka zagaye gidan, sauran sun shiga gidan sukayi awon gaba da shi.

"Basu yi harbi ba saboda gidansa na kusa da ofishin yan sanda."

Bayan dauke Murtala Maji Nasara, sai suka garzaya gidan Yusuf Ibrahim, wani babban ma'aikaci, inda sukayi awon gaba da shi.

A bangare guda, Mutane hudun da akayi garkuwa da su kusa da Zuma Rock dake daura da birnin tarayya Abuja sun dawo gida bayan kudin fansan miliyoyin nairan da iyalansu suka biya.

Masu garkuwa da mutanen da suka ajiye mutanen na tsawon kwanaki uku sun sakosu bayan karban kudin fansan N4.5 million. City News ta bada rahoto.

Daya daga cikin mutanen da aka saki, Muhammad Mustafa, dan kasuwa a kasuwar Wuse a Abuja yayinda yake magana da manema labarai ranar Laraba ya ce mutum daya daga cikinsu ya gudu da kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel