‘Yan kasuwa sun yi biris da umarnin NAFDAC, sun cigaba da sayar da Sniper

‘Yan kasuwa sun yi biris da umarnin NAFDAC, sun cigaba da sayar da Sniper

Kimanin watanni biyu kenan yanzu da hukumar NAFDAC ta haramta sayar da sniper da wasu magungunan kwari masu kama da ita a kasuwanni, sai ga shi kuma manyan kasuwannin Abuja sun karya dokar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito mana.

A yinkurin hukumar na rage yawan kisan kai da matasa ke aikatawa ta hanyar kwankwadar sniper ne ta haramta siyar da shi a kasuwanni da kuma hana shigowa da Dichlorvos wanda ake amfani da shi a gona.

KU KARANTA:‘Yan daba sun sake yin awon gaba da wani malamin makaranta a Kaduna

A cikin zancen da hukumar NAFDAC din ta fitar wanda ya samu sanya hannun shugaban hukumar, Farfesa Moji Adeyeye ta fadi cewa daga ranar 31 ga watan Agustan 2019 ba ta son ta sake ganin wannan maganin a kasuwanni.

Hukumar NAFDAC tare da kamfanin CropLife Nigeria sun aminta da samar da wani za a iya amfani da shi a gonaki a maimakon Dichlorvos. Sai dai kuma duk da cewa an samar da maganin mutane ba su raja’a a kansa ba.

A wani zagayen gani da ido da wakilin jaridar Punch ya kai a wasu manya-manyan shagunan Abuja kamarsu Shoprite ya samu cewa sun kiyaye dokar ta NAFDAC.

Amma kuma kasuwannin dake Abuja kamarsu, Dutse Alhaji, kasuwar Kubwa da dai sauransu dake birnin an samu har ila yau suna sayar da wannan maganin na sniper.

A wani labarin kuwa za ku ji cewa, wadansu ‘yan bindiga sun sace malamin makaranta da wasu mutum biyu a Birnin-Gwarin jihar Kaduna.

Ibrahim Nagwari ne yake shaidawa manema labarai aukuwar wannan lamarin inda ya ce da safiyar Laraba 16 ga watan Oktoba ne a abin ya faru.

https://punchng.com/traders-snub-nafdac-continue-sale-of-sniper/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel